Babu Wani Yunkurin Kasheni, Cewar Gwamnan Kogi, Bello

Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya karyata rahotonnin da ke cewa wasu ‘yan bindiga sanye da kakin sojoji su yi yunkurin kashe shi har sau uku kamar yadda kwamishinansa na yada labarai, Kingsley Fanwo ya yi ikirari.

An labarto cewa a ranar Lahadi ne dai kwamishinan ya fitar da wata sanarwa a madadin gwamnatin jihar inda ke cewa wasu sun yi kokarin kashe gwamnan jihar a hanyarsa daga Lokoja zuwa Abuja domin haifar da rashin tsaro a fadin jihar gabanin babban zaben gwamnan jihar da zai gudanaa a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

Fanwo ya ce, sau uku ana kai wa gwamnan hari, inda aka bude wuta ga ayarin tawagar motocinsa. Sai dai ya ce, jami’an tsaron gwamnan sun yi kokarin dakile aniyar maharan na yunkurin kashe gwamnan.

Sai dai, ‘yan awanni da fitar da labarin, a lokacin da gwamnan ya isa cikin Abuja, Bello ya karyata rahoton da cewa labarin na kanzon kurege ne kawai.

Da yake ganawa da ‘yan jarida a gidansa da ke Abuja wanda kuma aka yada kai tsaye a shafinsa na facebook, Gwamna Yahaya Bello, ya tabbatar da cewa an dai samu wata ‘yar gajeruwar rashin fahimta a tsakanin jami’an tsaron tawagarsa da wasu jami’an tsaron a wani shingen bincike kuma daga baya an shawo kan matsalar cikin ruwan sanyi.

Ya ce, “Muna hanyarmu daga Lokaja zuwa Abuja lami-lafiya daga bisani aka samu wata rashin jituwa da jami’an tsaron ayarina da wasu jami’an tsaro, amma cikin gaggawa muka tabbatar da an shawo kan matsalar. Tafiya ce muka yi cikin kwanciyar hankali kuma mun iso Abuja lafiya.

“Daga baya kuma na fara ji a kafafen sadarwar zamani cewa an yi kokarin kasheni. Balo-balo ina shaida wa ‘yan Nijeriya babu wannan batun na kashe ni Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi daga sojoji ko wani mutum na daban.

“Babu wani da ya yi kokarin kasheni ko wani daga cikin ‘yan tawagata.”

Ya shaida cewar jami’an tsaron da suke karkashin tawagarsa mutane ne masu ladabi da da’a. daga bisani gwamnan ya yi kira ga hukumomin tsaro da su fito su bincike abubuwan da ya faru domin hukunta duk wanda suka samu da laifi.

“Ni mutum ne mai biyayya wa doka da oda da kuma jami’an tsaronmu da nake matukar mutunta rayuka da dukiyar al’umma. Kuma, ni mutum ne mai girmama kakin jami’an tsaro, nake mutunta jami’an tsaron sojin Nijeriya da rundunar soji gaba daya, ‘yansandanmu da sauran hukumomin tsaro.”

Ya ce, a jiharsa ta Kogi dukkanin bangarorin tsaron suna gudanar da aikinsu bisa hadin guiwa da gwamnati wajen kyautata rayuwar al’umma ba tare da wata matsala ba.

“Don haka, ina kira ga jami’an tsaro da su bincika duk wani da aka samu da laifin rashin gaskiya a cikin ‘yan sanda ko wani bangaren na tsaro a hukunta mutum domin kare faruwar hakan gaba.”

Gwamnan ya jaddada cewar zuwa yanzu babu wata rashin fahimta a tsakanin jami’an tsaron da suka samu rashin jituwar domin an shawo kan lamarin cikin ruwan sanyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories