HISBA Ta Cafke Karuwai Da Masu Sayar Da Barasa 37 A Yobe

Hukumar tsaron HISBA, da haɗin guiwar hukumar NDLEA gami da jami’an ‘yan sanda a jihar Yobe, sun samu nasarar cafke mutum 37 da ake zargi da kasancewa a baɗalar karuwanci da sayar da Barasa a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Da ya ke ganawa da ‘yan jarida jim kaɗan bayan kamen mai riƙon muƙamin kwamandan Hisbah a jihar, Mohammed Murtala Goni Ahmed, wanda shi ne ya baje kolin waɗanda ake zargin a ranar Juma’a a caji ofis ɗin ‘yan sanda, ya ce, sun yi kamen ne a samamen da suka ƙaddamar a Zango, Maina Lodge, Ajayi, Bakin Kasuwa da kuma Last Bus Stop, dukka da suke cikin garin Damaturu.

A cewarsa, adadin waɗanda ake zargin su 37 da suka ƙunshi mata 17 da kuma maza 20 sun kasance ƙananan ‘yan mata da samari ne masu shekaru daga 15 zuwa 19 kacal.

Ya ce, “Bincike na gudana kan waɗanda aka kaman kuma an gano cewa mazan da aka kama da damansu suna sayar da kwayoyi har ma an kamasu da katan-katan 50 na barasa daban-daban.”

Sai dai kuma, wasu daga cikin waɗanda aka kaman da suka zanta da ‘yan jarida sun ce, an yi kuskure wajen kamasu domin su ba su aikata kowace irin laifi ba, sai dai wasu kuma sun nuna cewa tabbas sun kasance masu wannan laifin da ake zarginsu.

Maryam Umar, ‘yar shekara 19 a duniya, ta yi iƙirarin cewa, ta je Ajayi Joint domin sayen abinci ne aka cafketa.

Sannan, wata mace da ake zargi, Christy Peter, ta ce, ita da ƙawarta sun kasance a otel ɗin Maina Lodge domin sayen ruwa da kuma kayan marmari ne aka cafke su.

An naƙalto cewa mafi yawan waɗanda aka cafke ƙananan yara ne masu ƙarancin shekaru kuma an gano cewa su ɗin ba ‘yan asalin jihar Yobe ba ne domin sun fito ne daga jihohin Kano, Gombe, Borno, Bauchi, da jihar Filato wasu ma kuma daga Jamhuriyyar Nijar da Chaɗi suke.

Shi ma da yake zantawa da ‘yan jarida, kwamishinan kula da harƙoƙin addinai na jihar, Alhaji Yusuf Umar Potiskum, ya tabbatar da cewa, Hisbah za su ci-gaba da gudanar da nagartacce aiki domin tsaftace jihar, don haka ne ya bai wa jama’an jihar tabbacin cewa aikinsu bisa inganci suke yi.

Sai ya jinjina wa gwamnan jihar Mai Mala Buni bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da ɗa’a da ladabi a tsakanin al’ummar jihar.

Kwamishinan ya nuna rashin jin daɗinsa da harƙoƙin baɗala da ake samu a jihar da suka ƙunshi kesa-kesan shaye-shayen miyagun kwayoyi, fyaɗe, zubar da jarirai, inda a cewarsa, hukumar Hisba na ƙoƙari wajen tabbatar da da’a da ladabi a tsakanin al’umman jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories