Hukumar kwallon kafa ta Zambia ta gabatar da kasafin dala miliyan 2 don daukar kofin AFCON

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Zambia (FAZ) ya gabatar da kasafin dala miliyan 2 ga ma’aikatar matasa, wasanni da fasaha ta kasar domin halartar gasar cin kofin kasashen Afirka na 2023.

Shugaban FAZ, Andrew Kamanga ya bayyana kasafin a matsayin zuba jari ga Chipolopolo a daidai lokacin da kasar ke da burin daukaka martaba na lashe AFCON a Ivory Coast domin samun kyautar kusan dala miliyan 5.

Zambia ta dawo gasar AFCON a karon farko tun bayan shekarar 2015 inda take fatan lashe gasar a karo na biyu a tarihin gasar.

Zambia ta samu kanta a rukunin F na gasar tare da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Tanzania da kuma Morocco.

A halin da ake ciki, tsohon kocin Chelsea Avram Grant ya fara shirye-shirye tare da ‘yan wasa 30 a Lusaka inda ake sa ran zai bayyana sunayen ‘yan wasansa na karshe a ranar 1 ga Janairu kafin tashinsu zuwa Saudi Arabia don yin atisayen karshe.

A ranar 9 ga watan Junairu ne dai tawagar ta Chipolopolo za ta kara da Kamaru a wasan sada zumunta da za a yi a Jeddah, da kuma wani wasan sada zumunci da abokiyar karawar da ba a tabbatar da ita ba ranar 5 ga watan Janairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories