Lalacewar Muhalli: Yadda ‘Yan Mata Ke Kaurace Wa Zuwa Makaranta A Lokacin Jinin Al’ada

Daga Ogechukwu Victoria Ujam

A cikin kwalejin ilimi ta Yakubu Bauchi College of Islamic Studies (YBCIS), da ake ganin ana samun ilimi mai inganci, sai dai kuma akwai wani abu da ke kawo gagarumin cikas ga lamuran tafiyar harkokin karatun dalibai mata. Aisha Yusuf, wata daliba ce ‘yar SS1 a kwalejin, ta fuskanci rashin zuwa makaranta a lokacin jinin al’ada (Haila) na wata-wata sakamakon rashin kyawun yanayin makarantar.

Ko ba don komai ba, ko don kula da kiwon lafiyarta da tsafta, ba ta iya amfani da bayan gidan makarantar wajen saffara kanta a lokacin da take fama da jinin al’ada, ba ita kadai ba, bincike ya nuna mata da dama haka suke fama, wanda ala tilas suke fasa zuwa makaranta a irin wannan yanayin domin kiyaye lafiyarsu da tsaftarsu.

“A yayin da takwarorina suka dukufa wajen koyo, ni kuma na samu kaina a gida,” Aisha ta shaida, wacce lalacewar bayan gidan makarantar YBCIS ya ke kawo mata cikas ga cika burinta na samun ilimi. Wurin, ya kunshi lalacewa, babu kofofi, shinge ya ruguje, rufin ya lalace, da daidai sauran matsalolin da suke kawo cikas ga mata iya kula da tsaftar jikinsu a lokacin da suke jinin haila.

“Yadda mace za ta samu ta canza ‘Pad’ (abun tare jini) ma gagarata yake yi saboda rashin tsafta da munin wurin, kuma, na gama nazari, mafi alkairi ga kiwon lafiyata shi ne kawai na zauna a gida har sai na kammala jinin al’adar, hakan kuma na dakile mana kokarinmu na samun ilimi,” ta shaida.

Halin da Aisha take ciki bai zama wani sabon abu ba, wanda ana fama da irin wannan matsalar na tsawon shakaru a makarantu da dama kuma na kawo cikas ga harkar ilimi wanda har zuwa yanzu ba a dauki matakai a kai ba.

An kafa ta ne a shekarar 1995, WikkiTimes ta labarto cewa Yakubu Bauchi College of Islamic Studies (YBCIS) ta fara ne tun daga firamare na islamiyya har zuwa ga matakin sakandari da take kula da dalibai 1,500 a karamar hukumar Toro da ke jihar Bauchi.

Buga-bugar neman ilimi ga dalibai na kasancewa cikin yanayi mai ban wahala. Lalacewar muhallin koyo na zama babban damuwa wajen hana dalibai samun saukin samun ilimi. A wasu lokutan, daliban su na zama ne a kan kasa saboda rashin kujerun karatu yayin da wasu kuma ke zuwa abun shimfida daga gidajensu wato tabarma ko darduma domin shimfidawa su zauna domin daukar darasi. Wani abu mafi ban takaici shi ne yadda wasu azuzuwan ke fama da yoyon ruwa sakamakon yayewar rumfin azuzuwa ko bacinsu.

Kokarin shawo kan wadannan tulin matsalolin da dan majalisar da ke wakiltar yankin, Umar Muda Lawal hakan ya gagara cimmuwa. Shirin gyaran da aka shirya yi da sunan aikin mabaza, bai samu cimma nasara ba, illa iyaka an gyara dakin zana jarabawa, rukunin ma’aikata, da wasu ofisoshi guda biyu da ake yi wa kwaskwarima, a yayin da kuma matsalolin suke jibge ga yadda mata za su kula da jinin al’adarsu da tsaftar muhalli tare da sauran ababen more rayuwa da suke cikin gagari a makarantar ta YBCIS.

A shekarar 2021, ma’aikatar kimiyya da fasaha ta shirin ayyuka na shiyya, ta ware maguden kudade da yawansu ya kai miliyan 20 da niyyar gyara makarantar. Bayanin kwangilar kamar yadda shirin ayyukan shiyya (ZIP) ya nuna, an bayar da kwangilar gyaran ne ga kamfanin Debiro Integrated Service Limited.

Sai dai kuma, cikakken binciken da aka gudanar ya nuna cewa ba a kammala aikin ba kamar yadda aka tsammata, yayin da aka bar dalibai cikin yanayi marar dadi na koyon karatu.

Sannu a hankali, binciken da wakilinmu ya gudanar ta hanyar lalubo bayanin kamfanin Debiro Integrated Services Limited Suit a hukumar kula rijistan kamfanoni ‘Corporate Affairs Commission’ (CAC) da Nigeria check.ng portal, ya gano cewa kamfanin bai da cikakken bayani a safar, hakan ke nuni da cewa kamfanin bai gudanar da aiki yadda ya dace.

Dangane da dokoki da ka’idojin CAC, kamfanonin da basu gudanar da aiki (marasa aiki) su ne wadanda suka gaza bin sashi 417 – 424 na dokar kamfanoni ta 2023, musamman wadanda suka gaza biyan kudin harajin shekara-shekara.

Sashi na 417 na dokar ya cewa, dole ne, a kalla sau daya a shekara kowani kamfani ya gabatar da takardunsa ga hukumar. Rashin yin hakan na nuni da cewa wannan kamfanin bai amfani.

Binciken da wakilinmu ya gudanar a wurin ya nuna masa cewa hatta bayanan aikin da aka bayar da kwangilar nasa bai kammalu. Kawai, dakin zana jarabawa guda daya, da dakunan ma’aikata hade da ofisoshi guda biyu ne kawai ake kan musu kwaskwarima.

Sabanin hakan, sauran gine-gine (kantaga) da suka hada har da dakunan karatu, bayan gida (mazagayi) na fama da matsaloli ba tare da an gyara su ba, duk kuwa da cewa an fitar da kudaden da aka ware domin aikin. Sai aka gyara wuraren da ba su ma kai wadannan muhimmanci ga dalibai ba da harkar koyo ba.

Duk da kokarin da aka yi ta yi domin neman fayyacewa da karin bayani, Umar Lawal, dan maajalisa, ya ki bada amsa kiran waya da aka masa dangane da halin da kwangilar ke ciki. Kazalika, cibiyar kula da gine-gine ta Nijeriya NBRRI, da aka tuntuba ta hanyar bukatar neman bayanai ta tsarin FOI, sun ki cewa uffan kan aikin kwangilar da ke gudana.

Ziyarar binciken gani da ido zuwa wurin da aka yi, ya nuna cewa dalibai kusan 100 na zaune ne a kasa kuma cikin aji guda daya tak.

Wani malami da ya yi magana da wannan jaridar ta hanyar cewa kada a bayyana sunansa, ya yi bayanin cewa rashin wadatattun kayan aiki da na koyo da koyarwa na daga cikin dalilan da suke janyo ficewar dalibai daga makaranta.

Mataimakin shugaban makarantar YBCIS, Jamil Abubakar Gumor, ya yarda kan cewa munin yanayin muhalli na shafar shigar dalibai makaranta. Ya yi bayanin cewa tun bayan wata annobar gobara da ta faru a shekarar 2020 ta lakume dakin zana jarabawa, kuma Mista Lawal shi ne ya yi kokarin gyarawa a shekarar da ta biyo baya. Duk da kokarin da aka yi ta yi ga al’umma da su shigo da ‘ya’yansu cikin makaranta, amma munin muhalli da lalacewar azuzuwan karatu na sanyaya guiwar dalibai daga zuwa makaranta, hakan ke janyo mummunar nakasu ga shigar dalibai makarantar.

A bisa kididdigar shigar dalibai makarata, rukunin firamare, da can baya a kalla dalibai 1,500 ne suka shiga, amma yanzu sun ragu sun dawo 500.

Mista Gumor ya koka da rashin samar da ababen more rayuwa, ya kuma yi nuni da yadda kashi 90 cikin 100 na gine-ginen makarantu ke tabarbarewa, lamarin da ke haifar da kalubale ga malamai da su kansu dalibai.

Mummunan halin da makarantar ke ciki ya zama abin damuwa ga mazauna kauyen, wadanda ke nuna damuwa game da lafiyar ‘ya’yansu. Wata mazauniya mai suna Libabatu Adams, ta bayyana damuwarta kan tsarin, inda ta ba da labarin rugujewar ginin makarantar shekaru biyu da suka gabata.

Ta bayyana fargaba, musamman ga dalibai mata da ba su da wuraren da suka dace a lokacin al’adarsu. Wata mazauniyar da ta nemi a sakaya sunanta, ta koka kan matsalar kudi da ake ta fama da ita wajen kula da ‘ya’yanta mata saboda matsalar lafiya da aka samu daga makarantar. Ta kuma jaddada a maimakon ta bari diyarta ta gamu da cutuka sakamakon rashin kyan makarantar, ta gwammace ta cire diyarta daga YBCIS, inda ta yi nuni da gurbacewar yanayin ilimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories