JTF Ta Cafke Mutum 135 Kan Zargin Addabar Abuja Da Manyan Laifuka

Jami’an tsaron da ke ƙarƙashin haɗakar jami’ar tsaron (JTF), sun cafke mutum 135 da ke zarginsu da aikata manyan laifuka nau’ika daban-daban da suke addabar birnin tarayya Abuja (FCT).

Da ya ke ganawa da ‘yan jarida a ranar Alhamis a Abuja, kwamishinan ‘yan sanda da ke kula da birnin tarayya Abuja, CP Haruna Garba, ya ce, “Idan za ku tuna dai ministan birnin tarayya, Nyesom Wike ne ya ƙaddamar da tawagar haɗakar jami’an tsaro domin daƙile kowace nau’ikan ayyukan ta’addanci a cikin birnin tarayya, musamman ‘yan daba da suke addabar kwanciyar hankalin FCT.”

A cewarsa, a yunƙurin tawagar na cimma nasara da suka haɗa da tawagar sojoji, ‘yan sanda, NSCDC da kuma DTRS sun ƙaddamar da samamen cafko ‘yan ta’adda a maɓoyarsu da wuraren da suke boye a irin gine-ginen da ba a kammala ginawa ba, dazuka da sauran wuraren da ɓata garin ke ɓuya.

A faɗinsa, a bisa wannan samamen, sun samu nasarar cafke mutum 135 da suke zargi da aikata manyan laifuka daban-daban a Kwali, Dutse Alhaji, Mpape, Karu, AYA, Nyaya, Karmo, Karshi, Kuje, Airport Road, shataletalen Berger, Jabi, Orozo da kuma Mararaba.

“Daga cikin, mutum 75 da muke zargi an gurfanar da su a gaban kotuna daban-daban, yayin da kuma 65 aka yanke musu hukuncin biyan tara da suka kama daga naira N5,000 zuwa N7,000, sauran 10 kuma an yanke musu hukuncin yi wa jama’a hidima.”

Kwamishinan ya ƙara da cewa, “Masu laifi 39 da aka gurfanar a ranar Alhamis suna kan fuskantar tuhuma kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar aka kammala gudanar da bincike.”

Ya ce, takwas daga cikin waɗannan da ake zargin, mutum 8 sun kasance ana zarginsu da shiga ƙungiyar wafce da ke amfani da wuƙaƙe da sauran abubuwa wajen satar motocin jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories