Sarkin Bauchi Ya Kai Ziyarar Bazata Kasuwanni, Ya Gargaɗin ‘Yan Kasuwa Da Su Ji Tsoron Allah

Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu, ya kai ziyarar bazata a cikin kasuwannin da suke faɗin masarautar Bauchi inda ya yi mu’amalar cinikayya a tsakaninsa da ‘yan kasuwa tare da janyo hankalinsu da su ji tsoron Allah a kowani lokaci.

Sarkin wanda ya bibiyi yadda ake auna kayan masarufi da yadda wasu ‘yan kasuwa ke tauye Mudu, ya sanya da kansa aka tara masa Mudunan awu inda ya nazarci waɗanda aka tantance da waɗanda ake amfani da su ba bisa ƙa’ida ba.

Sarki Rilwanu dai ya ziyarci kasuwar Muda Lawal, Wunti kana ya nausa zuwa kasuwar kauye ta mako-mako da ake ci duk ranar Lahadi a Durun.

Wakilinnmu ya labarto cewa Sarkin ya kuma yi sayayyan kayayyakin buƙata da dama domin ya gane wa kansa yanayin da al’umma ke sayen kayan masarufi a hannun ‘yan kasuwa.

Kazalika, ya tambayi ‘yan kasuwa da masu sayen kayayyaki halin da suke ciki dukka domin jawo hankalin kowani ɓangare da ya riƙe gaskiya cikin harkokin rayuwa domin sauƙaƙa wa jama’a matsatsin da ake ciki.

Dakta Rilwanu ya ce, bai dace a yanayin da ake ciki na tsadar kayan masarufi kuma ya kasance ‘yan kasuwa ba su cika ma’auni ba, ya jawo hankalin su kan yin abubuwan da suka kamata domin rayuwa ta ke inganta.

Sarkin wanda shi ne shugaban majalisar sarakuna na jihar Bauchi, ya buƙaci ‘yan kasuwa da su rage farashin kayan masarufi domin samun sauƙin rayuwa lura da halin matsatsin tattalin arziki a yanzu.

Wasu ‘yan kasuwa da dama da suka tofa albarkacin bakinsu, sun nuna jin daɗinsu da farin cikinsu ga irin ziyarar da Sarkin ya kai musu, suna masu nuna cewa hakan zai ƙara musu ƙumajin cewa ya dace su cigaba da yin abubuwan da suka dace a kowani lokaci domin mahukunta na bibiyar abubuwan da suke yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories