Ba Yafe Wa Kwastomominmu Bashi Muka Yi Ba, Tangarɗar Na’ura Ce – MTN

Daga Halima Lukman

A ranar Asabar ne kamfanin sadarwa ta MTN ta samu dangarɗar na’ura da dukka kwastomominsu da ake bin bashin kati da data asusun nasu ya nuna cewa an biya alamin kamfanin ya musu yafiyar gata.

Mutane masu amfani da layukan MTN sun bayyana farin cikin su ta hanyar dauka a hoto da sanya wa a kafar sada zumunta na facebook.

Sai dai MTN ta ce, “Hakan da ya faru matsala ta na’ura ce,” ta kara da cewa, idan kwararrun injiniyoyinsu suka shawo kan matsalar to fa duka kudaden da ya nuna an biya zai dawo yadda yake a matakin bashi.

Sannan ta ce ma’aikatan ta na aiki tukuru wajen gyara matsalae kuma su na kara bada hakuri akan wannan tsautsayin da ya faru.

Wikkitimes ta bayyana wasu da ke ta tofa albarkacin bakinsu a kafar sada zumuntan na X da Whatsapp, sun hada da alameenMS inda ya ce “MTN kenan ba amana ba za ku yi kirki ba ko sau daya”.

Wani mai suna @princedmax ya ce “shashashun campany har nawa kuke son samu a Nigeriya ……da me zaku sakawa mutane a cikin wahalar nan da ake ciki”.

A WhatsApp kuma Fatima Muhammad Bello ta ce “Su MTN ba saban ba an biya bashi, da na sani da na ci ya fi haka”.

Daga karshe kafar ta ce “Y ‘ello MTN Nigeria, mun samu matsalar kafar sadarwa ta har ya kai ga biya wa mutane basukansu, wannan matsala ce da ya auku amma za mu gyara kuma kowa bashi shi zai dawo.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories