Shin Da Gaske Hoton Da Ke Yawo A Soshiyal Mediya Gawar Dogo Giɗe Ne

Rahotannin da ke ta yawo a kafafen soshiyal mediya a safiyar yau inda ake ta yaɗa wani hoto da cewar shi ne Gawar Ɗan bindiga Dogo Giɗe.

Bayyanar wannan hoto ya sa jama’a da dama nuna murna da farin cikin su inda suke ganin haka wata nasara ce ta kawo ƙarshen Ta’addanci,a ɗayan ɓangaren kuma wasu sun nuna shakku game da hoton inda suke ganin kamar ba fuskar Giɗe ba ne ake nunawa a matsayin gawar sa.

 Jim Kaɗan Bayan fitar wannan labari sai wani mai amfani da kafar Sada zumunta m Abdallah habeeb ya wallafa a shafin sa inda ya karyata wannan hoto da ake alakan ta shi da Dogo Gide.

 Inda ce“Dan Allah kafin mu yaɗa labari mu tabbatar mun tantance gaskiyar sa game da hoton da ke yawo wannan hoto ba na Dogo Giɗe ba ne,wannan hoto na wani mutum ne ana ce masa Ɗan Asabe wanda aka fi kira da Sabebe.Tabbas rahotanni sun bayyana mutuwar Dogo Giɗe amma wannan hoto da ke yawo ba nasa bane.”

Sabebe ya kasance ɗan wasan ƙwallon ƙafa a jihar Kaduna wanda Allah yayiwa rasuwa a sakamakon haɗarin mota.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories