Yadda Ake Yawan Mace-mace Ya Kamata Ka Sawa Zuciyar Ka Salama – Mama Tambaya Ga Zango

A cigaba da ka-ce-na-ce da ke cigaba da faruwa tsakanin Adam Zango da abokan sana’ar sa a Kannywood,ita ma Mama Tambaya ba a barta a baya ba wajen maida martani.

Jaruma Mama tambaya a faifan bidiyo da ya bayyana ta fito ta tofa na ta albarkacin baki game da lamarin.Mama Tambaya a nata furucin ta fito tana yiwa jarumi Zango nasiha da kuma faɗakarwa tana mai cewa:

”Ɗana Zango Allah ya maka albarka,a matsayina na uwa kuma kaka ɗan Allah ɗan son Annabi ina mai baka hakuri ka yafe ka bar wannan maganar,Karka manta da ita rayuwa babu wanda zai iyawa mutum sai Allah.”

”Dan Allah Dan Allah ka yi haƙuri Ɗana! Kayi haƙuri Ɗana!”

Mama tambaya ta cigaba da cewa Kaduba kaga yadda ake yawan Mace-mace,ko ina mutuwa kawai ake yi ta kuma ƙara da cewa kar ka manta in mu ne yau ba mune gobe ba,ta ƙara da bashi hakuri.

A ƙarshe ta yi godia tare da bayyana cewa wannan faɗa da ta yi masa zata gani ko tana da matsayin da ta isa ta hana shi abu ya gamu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories