Muhimman Sirrika Da Ke Ƙarawa Aure Ƙarko

Aure wani Babban lamari ne da ke faruwa tsakanin mace da Namiji ,a inda waliyyai za su ayyana sannan dunia kuma ta sheda su a mastayin mata da miji.

Malam Bahaushe ya ce zo mu zauna zo mu saba kuma an sani cewa duk wata zaman takewa musamman na aure yana cike da ƙalubale amma idan aka kauda kai sai zaman ya dore a yi shekaru kamar na dabino ana rayuwa tare, Amma ta ya ya hakan zata kasance?
Ga kadan daga cikin sirrikan da ke karawa aure karko

-Zaman Hakuri a duk inda aka ambaci kalmar hakuri to fa babbar lamarine,hausawa sukace hakuri maganin zaman dunia,haka zalika a gidan auren ma hakuri shine babban jigo,uwar gida da me gida ya kamata su san cewa hakuri a zamantaekwa yana da matukar amfani ,da kawai da babu uwargida ta kasance mai hakuri da duk abinda ya sami,tun daga kan abinci zuwa sauran abubuwan rayuwa.

-Fahimtar juna yana da matukar tasiri a zaman aure hakan na kara zaman lafia.

-Kauda kai idan aka ce kauda kai ana nufin ma’aurata su kasance suna dagawa abokan zaman su kafa,misali miji ya dawo mata bata gama abinci ba idan har ya kasance kullum tana kokarin kammalawa a kan lokaci to ya kamata a ce na rana daya maigida ya daga kafa ya kauda kai kar ya ce zai yi fada ko masifa.Haka itama uwargdia ta kasance mai kauda kai ga hidimar miji ba komai ne zata sa ido sai ta sani ko ta ji ba.

-Boye sirri a zaman aure yanada matukar tasiri miji ko mata ya kamata su yi kokarin ganin suna tattaunawa mastsalolin su da damuwar su ga juna hakan na kara dankon soyayya da kuna zaman lafia.

-Girmama iyaye da ‘yan uwan juna ma’aurata ya kamata su fahimci cewar girmama ‘yan uwan juna yana da matukar tasiri a zaman takewae juna.ya kasance babu raini iyayensa ki dauke su kamar ba ki haka shima naki ya zama yana musu kallon nasa iyayen.

-Hakuri da akwai ko babu wannan zai fi karkata ne ga uwargida ,ya kasance uwargida ta san cewa a zamantakewar aure akwai lokacin da halin rayuwa zai sauya walau dadi ko kuma akasin haka,to a duk wanda uwargida ta tsince kanta a ciki ya kamata ta jajirce ta zama mai hakuri ta kasance mai karfafawa miji gwiwa,dan abunda ya kawo karki raina karba da murni ki sarafa muku kuyi amfani dashi sannan kiyi addu’ar Allah ya kawo na gaba ,Allah kuma ya buda masa.irin wadannan halayyar addu’a da kuma hakuri da abinda aka samu su kan kara so da kauna da kuma zaman lafia mai dorewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories