Ko Kanawa Na Buƙatar Gadar Sama A Yanzu Kuwa?

Tsigar jiki na har tashi ta kan yi idan na tuna shekarun baya lokacin ana tsaka da Boko Haram, yadda idan ka fito titin Zaria Road da rana tsaka sai ka ga motoci ba su fi a kirga ba, da mutane dai-dai a gefen titi. Amma kuma na kan yi wa Allah godiya ganin yadda wannan lamari ya zama tarihi.

Mutanen Kano sama da miliyan 20 sun dukufa da addu’o’i da bada hadin kai wajen ganin cewa Boko Haram ba ta sami gindin zama a Kano ba, kuma yanzu haka an dawo da hadar-hadar da aka san Kano da ita. A halin da ake ciki yanzu haka, jihohin Kano da Jigawa kadai ke zaune lafiya a cikin jerin jihohin Arewa maso yamma daga masifun Boko Haram, masu sata da garkuwa da jama’a da yan tada kayar baya. Wannan ba karamar ni’ima ba ce, amma abin takaici mun gagari yin amfani da wannan dama, ganin cewa wasu wurare su na son su yi noma amma sun kasa saboda tashe-tashen hankali. Amma mu a Kano Allah ya albarkace mu da dam-dam har guda 22 wadanda su ke kwance su na barci har da minshari, yayin da abinci ya gagari al’ummomi kuma gwamnatoci na ta barna da kudaden jama’a a ayyuka mara sa fa’ida.

Lokacin gwamnati da ta gabata, a ka fito da tsarin baiwa manoma rance na CBN, amma babu jihar da a fadin Najeriya ta ci moriyar shirin sama da jihar Legas. Domin sun garzaya jihar Kebbi inda su ka hada hannu da gwamnatin jihar wajen yin noman shinkafa su na kaiwa jihar su. Kuma wannan lamari yadda su ka ga fa’idarsa ya sa sun kirkiri yin kamfani nasu na kansu na shinkafa. Wannan kamfani, wato na Imota ya kasance kamfanin sarrafa shinkafa mafi girma a fadin Afirka, kuma na uku mafi girma a duk fadin duniya. An gina kamfani a kan hecta 22 (a yankin da ke faman karanci kasar noma) kuma a na sa ran a duk shekara wannan kamfani zai samar da buhunan shinkafa na 50kg guda miliyan 2.8, tare da samar da ayyuka na kai tsaye guda 1500 da wasu ayyukan da ba na kai tsaye ba guda 254,000.

Bayan tabargazar gwamnatin Tinubu na cire tallafi, wanda tsari ne da zai ci gaba da bautar da talaka ya tallafi manya, saboda an karbe duk wata sa’ida da talaka ke samu a jikin gwamnati kuma gwamnatocin tarayya da na jihohi sun ci gaba da samun makudan kudaden kashewa fiye da na baya. Gwamnatin Sanwo-Olu a Legas ta yi hobbasa wajen kawo wa talakawanta sauki ta hanyar rage kudaden sufuri da kashi 50% na motocin gwamnati, da kuma kaso 25% na bas-bas din gari. Sannan sun sayi kayan abinci domin rabawa gidajen marasa karfi guda 500,000 wanda aka rarraba a fadin jihar.

Kada a ce ina yi wa Sanwo-Olu kamfe bari na koma kan mau’du’in mu. Bayan shekaru takwas da gwamnatin Ganduje ta bata a jihar Kano ba tare da wani abin a zo a gani na gina al’umma irin wanda Legas ta yi ba, mutane da dama sun yi dafifi wajen korar gwamnatin da kuri’a, kuma bayan Abba ya ci zabe murna ta karade ko’ina ana wa juna sam-barka saboda tunanin cewa gwamnatin Kwankwasiyya za ta baje kolin ayyuka na raya kasa da mutane. Amma abin takaici gwamnatin na shigowa a cikin sati uku su ka kama rusau wanda ba’a taba ganin irinsa a Najeriya ba, wanda wata kididdiga ta nuna ya janyowa jihar asarar biliyan 226.

Ba don hukuncin bagatatan na kotun zabe wanda ya soke nasarar Abba Gida-Gida ba, Allah kadai ya san ina wannan asara za ta tsaya. Sannan kuma ita kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kotun zaben. Wannan lamari ya jawo dole aka tsayar da rusau kuma hatta harkokin gwamnati su ka kusan tsayawa cik. Aka bar yan Kwankwasiyya da muzurai da al-qunut da jan carbi. Allah cikin hikimarsa sai ga shi Kotun Koli ta dawowa da NNPP nasararta, amma dai kusan shekarar babu wani abin a zo a gani da aka tsammata saboda wannan tsaiko na shari’a.

Ban cika goyon bayan surutan Sunusi Lamido ba, amma a lokacin da ya soki shirin Ganduje na kashe dala biliyan 1.8 domin gina hanyar dogo na cikin gari, wato metro, daga Bata zuwa Dawanau, na yi murna saboda akwai abubuwa a wancan lokaci mafiya mahimmanci. Koda ya ke wannan suka ita ta jawo masa rasa kujerar Sarkin Kano daga karshe, amma dai kuma sukar ta amfani jama’a domin ba’a kashe da wawushe musu kudade ta hanyar da ba ita su ke bukata ba.

Shi ya sa na yi tsammani, cikin shukurar da Gwamna Abba Kabir zai nuna wa Allah ya kuma saka mana shine ya bijiro da ayyuka wadanda za su amfani mutane. Kash! Sai ga shi aiki mafi girma na farko da gwamnatinsa ta sahale shine na gina gadojin sama guda biyu a birnin Kano. Wannan aiki Allah ya sani ba shi Kanawa ke bukata a yanzu ba.

Domin idan ka zana wata da’ira a kwaryar birnin Kano wadda zata fara daga kan gadar Gidan Murtala, ta yi arewa ta titin Ibrahim Taiwo, ta ratsa Murtala Muhammaed Way zuwa Katsina Road ta kewayo ta Muhammadu Buhari Way ta dawo Buk Road ta hade daga inda ta tashi a gidan Murtala, akwai gadojin sama guda 8 rigis. Ya Ilahi mu na bukartar karin biyu a kan wannan daira? Yayin da titin Kurna wanda ya ke daya daga cikin mafi cunkoso a jihar, kuma wanda ya fi shekaru 40 ba a fadada shi ba. Banda wasu gwamman kananan tituna a kwaryar birni da basa biyuwa ta dadi, da kuma daruruwa a kauyuka dake Local Government kusan 40?

Kanon da ke da Dam-Dam har 22 amma kwaya daya cikinsu ake morar kashi 40% dinsa yayin da sauran ke kwance su na barci da minshari, amma talakawan da ke kewaye da su na cikin bakin talauci? Ka san buhu nawa na shinkafa, alkama, tumatur da kifi da za’a iya nomawa da wannan biliyan 30 a wasu daga cikin wadannan dama-damai? Banda aikin yi da zai iya samarwa, tare da haraji da gwwamnati za ta samu, banda abinci da zai samarwa al’umma da kudaden kasar waje?

A yan kwanakin nan Kano ta dauki zafi saboda bigibagiron murabus din da Daurawa ya yi, domin kuwa idan ba bigibagiro ba, ai takarda aka ba shi ta aiki, kuma ita ma ta ajiye aiki ai rubuta ta a ke yi. Amma saboda dama manufar ita ce a harzuka tunanin mutane, duk wani malami, ba a Kano kawai ba a duk fadin arewa, kalilan ne ba su tofa albarkacin bakinsu ba cikin dambarwar. Haka nan jama’ar gari kowa ya zama mai sharhi. Amma wa ka ji ya fito ya soki lamarin ginin wannan gadoji a wannan lokaci da mutane ba sa iya cin abinci? Idan a wasu wuraren ne jama’ar gari sai sun yi zanga-zangar haka, kungiyoyi su kai korafi majalisa, manyan malamai su hau mimbari, kafafen watsa labarai sun sami abin tattaunawa. Amma tsit ka ke ji. Matukar shugabanni za su zama bukatarsu ba ta al’umma ba ita ce a gaba, malamai su zama yan kasuwar akida, talakawa jahilci da talauci ya baibaye su, to babu fa abinda ba zai iya faruwa ba.

Jihar Kano nan da yan shekaru kadan, yawan jama’arta zai haura miliyan 40, kuma a yanzu haka da zaka bi titin Zaria Road zuwa Kurna tsakanin karfe 1-2 na rana, idan ka ga dandazon yan mata da ke komawa gidaje daga makarantu wallahi sai gaban ka ya fadi domin akasarinsu nan da shekaru 3-4 duk za su zama uwaye sun fara haihuwa. Ya Ilahi me ake musu tanadi, gadojin sama? Banda tashin hankalin almajirai da ke tururuwa a kullum su na kwararowa cikin birnin Kano. Duk inda ka ratsa a cikin unguwanni da lunguna sai ka rika jin muryoyi na ban tausayi su na cewa “Ina sadaka iya…iya wallahi yunwa na ke ji” wallahi ko ba ka taba haihuwa ba sai zuciyar ka ta karye kuma ka yi tir da wannan tsari da ake sako yara har yan shekara 4 bara.

Shin don Allah masifar Boko Haram ba ta isa ta sa yan Arewa mu farka ba? Wallahi rami mu ke dosa, kuma kowannenmu na da hannu a cikin yanayin da muka sami kanmu, amma dai dole shugabanci shine zai dora mu a saiti. Allah ya bamu komai amma mun rasa komai? Kwarai kuwa domin yankin arewa ya fi kowa yawan jama’a, ma’adinai, filayen noma, rafuka da dama-damai, amma mun ciri tutar fin kowa talauci a duniya? Allah ne ya sa mana ko kuwa mu muka sakawa kanmu? Allah ba zai cece mu ba fa, sai mun ceci kanmu.

A karshe ya kamata wannan gwamnati ta Kwankwasiyya ta ci sunanta kuma ta yiwa talakawa ramakon halaccin da su ka yi mata wajen bijiro da ayyuka da zasu taba rayuwarsu kai tsaye. A yanzu babu abinda ke wahalar da kowane talaka irin abincin da zai kai bakinsa, don haka don Allah mai girma gwamna ka karkata ayyukan ka wajen inganta yadda za’a samar da abinci a wannan jiha. Ka dubi yadda Legas, jihar da ba ta da kasar noma amma a yau ta hayi filayen noma a Kebbi kuma ta samar da masana’antar shinkafa wadda babu irinta a Afirka. Wasu yankuna yau a arewa su na son yin noman, amma rashin zaman lafiya ya hana su, yaya mu da Allah ya albarkace mu da zaman lafiya, filayen noma, koguna, dam-dam da tulin marasa aikin yi a karkashin gwamnatin da ake gani ta jama’a ce, za’a kashe biliyan talatin wajen yin gada a birni, bayan rusa gine-gine na biliyan 226 a cikin shekara guda? Idan da biliyan 250 din nan an saka su a noman shinkafa, ba sai mun doke kowacce jiha a fadin kasar nan ba? Don Allah gwamna a sauya tunani, kuma shekaru 4 kamar yanzu ne. Allah ya baka iko.

Ali Abubakar Sadiq ya rubuto daga Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories