Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Ya Kiyaye A Watan Ramadana

Watan Ramadan wata ne da dukkan Musulmi a faɗin duniya ke ƙauracewa ci ko sha sanann kuma su ke sadaukarwa da kuma Tuba izuwa ga Ubangiji.Dukkannin musulmi suna maraba da zuwan wannan wata domin wata ne da ke tattare da albarkatu daban daban.

Akwai abubuwa daban daban da dukkan Musulmi zai kiyaye domin cikar azumin sa waɗannan abubuwa su ne:

Ana so musulmi ya sarrafa idanun sa daga kallon haram,yawan kallace kallace na lalata azumi.

Ci ko Shan Abun Maye Shan wani abu da ake so musulmi ya ƙauracewa domin yin hakan na lalata azumi.

Ƙauracewa Jima’i Yin jima’i ko dafuwa a lokutan azumi haramun ne.  Saboda Ma’aurata ana so su kauracewa duk wani nau’i na kusanci, waɗanda suka haɗa da sumbata da runguma, yayin Azumi.

Gulma ko Cin Naman watan Ramadan lokaci ne na natsuwa, tunani, tausayi, da kuma ƙauracewa duk wani aiki haram. Maganar wani,Yaɗa jita-jita abubuwa ne da ake so musulmi ya ƙauracewa domin kuwa yana lalata tare da rushe ladan mai azumi.  Wajibi ne musulmi ya kiyaye harshensa a wannan wata.

Shagaltuwa Duk da yake ba a hana nishaɗi ba,amma ana so musulmi kar ya shagala sosai wanda ya wuce ƙima wanda hakan na iya hana musulmi rabauta da rahama.

Rashin Sallah da sauran Ibadu Azumi ba wai kamewa daga ci da sha kawai ya yi hani ba,watan Ramadan ya ƙunshi hadda ba da himma wurin ibada saboda haka Yin watsi da sallolin farilla ko barin ayyukan ibada a cikin wannan wata hakan na rage ladar wannan azumi.

Ɓata lokaci a kallace -kallace Hakan ya kamata Musulmi ya kiyaye domin kuwa ana so mai azumi ya yawaita ji da kuma kallon karatuttuka da tafsirai.

Cin abincin Wuce Ƙa’ida hakan ba dai dai bane ana so musulmi ya ci abinci dai-dai misali ,kar ya ci abincin da zai kasa aikata sauran Ibadu.

Sadaka da Kyautatawa ana so a watan Ramadan musulmi ya kasance mai tausayi da tausayawa , Sadaka ga mabuƙata. Haka kuma ana so Musulmi su kasance masu yin aikin agaji da kuma tallafawa sauran al’umma masu ƙaramin ƙarfi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories