Al’ummar Garin Bini Sun Tsere Zuwa Fadar Gwamnatin Zamfara Don Neman Mafaka

Daruruwan mutanen ƙauyen Bini da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara sun yi wa gidan gwamnatin jihar Zamfara dirar mikiya a ƙoƙarin su na Ceton rayukan su.

 Mazauna ƙauyen waɗanda akasari mata da ƙananan yara ne sun tsere zuwa fadar gidan gwamnatin ne biyo bayan janye jami’an tsaro da aka yi daga yankin.

Wani magidanci a cikin masu tserewan mai suna Malam Umar Salisu ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN cewa dole ne ta sa suka gudu daga mahaifar su saboda an anje jami’an tsaro daga wurin .

 “A da, akwai jami’an soji da ke sintiri a ƙauyenmu. Wasu daga cikinsu ƴan bindiga  sun kashe su yayin da sauran da suka rage kuma aka janye su a ranar Lahadi.  Yanzu dai a halin da muke ciki babu jami’an tsaro a yankinmu. Don haka ne muka yanke shawarar ɗaukar iyalan mu zuwa gidan gwamnati don neman agaji cewar Salisu.”

A cigaba da bayyana irin halin da suke ciki Hajiya A’isha Usman ta bayyana irin rashin kwanciyar hankali da mutanen yankin ke ciki.

 “Mun damu matuka Muna samun barazanar kawo hare-hare daga ƴan fashi a kullum. Babu jami’an tsaro da za su kare mu.  Muna neman gwamnati ta duba mu, ” in ji ta.

Da yake jawabi a madadin gwamnatin jihar, kwamishinan kimiyya da fasaha, Alhaji Wadatau Madawaki, ya bayyana cewa yan bindigar na cin karen su ba babbanka ne saboda gwamnati ta ki zaman tattaunawa da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories