Sojojin Najeriya Sun Bankaɗo Wani Gidan Burodi Mallakin ISWAP A Maiduguri

A wani rahoto da BBC ta wallafa ta ruwaito cewar Dakarun sojin Najeriya sun bankaɗo wani gidan gasa burodi na ƙungiyar ISWAP a garin Maisani, da ke karamar hukumar Damboa na jihar Borno.

A cewar wasu bayanan sirri da wani masani kan ƙungiyoyin ta’addanci, Zagazola Makama ya fitar ranar Litinin, ya ce haɗin gwiwar dakarun bataliya ta 199 da kuma rundunar tsaro ta JTF Su ne suka gano wannan wuri yayin wani samame da suka kai kan maɓoyar ƴan ta’adda a ranar Lahadi.

Zagazola ya wallafa cewar”Majiyoyi sun bayyana cewa an yi nasarar lalata gidan burodin tare da ƙwato kayayyaki irin su manyan injunan samar da hasken wutar lantarki guda biyu, abin gasa burodi da kuma wasu kayan haɗin yin burodin,”

Rahoton ya cigaba da cewa an gano wurin  ne a lokacin da sojoji suka kai wani samame na tsawon mako ɗaya a ƙoƙarin su na kakkaɓe ƴan ta’dda daga yankunan dajin Timbuktu Triangle, da sauran yankuna da suka haɗa da Talala, Ajigin, Dusula, Abulam da kuma Gorgi, kasancewar su wurare masu haɗari ƴan tanada ke fakewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories