Auren Zumunci: Sarakunan Kano Da Bichi Za Su Haɗa Ƴaƴansu Aure

Masarautar Kano da ke Arewacin Najeriya ta bayar da sanarwar daurin auren Yarima Sanusi Aminu Bayero (Halifa) da kuma Gimbiya Rumana Nasir Bayero.

Yarima Sanusi Aminu Bayero ya kasance ɗa ne a gurin Sarkin Kano Aminu Ado-Bayero ita kuma Gimbiya Rumana Nasir Bayero ƴa ce ga Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Za a daura auren ranar Juma’a 26 ga watan Aprilun nan a fadar Sarkin Kano da misalin karfe 10 na safe”.


Sarkin Kano Aminu Ado-Bayero yaya ne ga Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero, kuma sun zama sarakunan masu daraja ta ɗaya bayan da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta cire Muhammadu Sanusi II tare da ƙirkiro sababbin masaratu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories