Ko Yahya Bello Ya Gurfana Gaban Kuliya Ko In Ajiye Aiki-Shugaban EFCC

Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati, EFCC, Ola Olukoyede, ya sha alwashin bin diddigin almundahanar Naira biliyan 80.2 da ake zargin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi.

 Mista Olukoyede, ya sha alwashi ne yayin zantawa da manema labarai a hedikwatar hukumar, inda ya ke cewa indai Yahya Bello bai Gurfana gaban kuliya ba zai ajiye aiki.

“Idan ban kawo ƙarshen binciken da ake yi kan Yahaya Bello ba,tabbas zan mika takardar murabus ɗin a a matsayi na na shugaban EFCC,” in ji Mista Olukoyede.

 Haka kuma ya alwashin cewa duk wadanda suka kawo cikas ga kama Yahya Bello suma bincike zai biyo ta kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories