An Sami Ɓallewar Gidan Yarin Suleja, Fursunoni Da Dama Sun Tsere

Rahotanni da ke fitowa daga gidan yarin Suleja ta jihar Neja sun bayyana cewa an sami guduwar fursunoni aƙalla 119 .

Fursunonin sun tsere daga gidan gyaran halin ne sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da ya yi sanadiyyar rusa wani bangare na katangar gidan yarin a jiya Laraba.

Bayanai sun bayyana cewar an yi nasarar dawo da wasu  fursunonin yayin da jami’an tsaro da jami’an gidan gyaran halin ke ci gaba da bin lungu da saƙo don ganin an bankaɗo sauran waɗanda suka tsere.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories