Ƴan Rakiyar Amarya Sun Kashe Ɗan Bindiga A Zamfara

Ƴan uwan Wata amarya tare da taimakon wasu fasinjoji sun yi nasarar dakile yunƙurin yin garkuwa tare da kashe wani ɗan bindiga.

 A cewar PRNigeria, lamarin ya faru ne a lokacin da ƴan bindiga suka yi wa iyalan amaryar da wasu matafiya kwanton bauna a hanyar Talata Mafara zuwa Gusau a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ƴan uwan amaryar ke hanyar su ta zuwa siyayan kayan aure a Kano. Sai kwatsam ƴan bindiga ɗauke da makamai suka far musu .

 Wani ganau da ya zanta da PRNigeria ya bayyana cewa lokacin da ƴan bindigan suka far musu sai fusatattun, fasinjojin suka kwace bindigogin AK-47 guda biyu daga hannun maharan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories