Asibitin Da Ake Rade-Raɗin Dogo Giɗe Ya Mutu,Sun Bayyana Gaskiyar Lamari

A yayin da ake ta ka-ce-na-ce game da mutuwar shugaban ƴan bindiga Dogo Gide, hukumar gudanarwar asibitin Relance Specialists dake Sokoto,inda a nan ne aka yi ta yaɗa cewar Giɗe ya mutu sun fito sun musanta zancen.

 Idan ba a Manta ba amakon da ya gabata ne aka yi ta yaɗa labarin cewar Dogo Giɗe Ya mutu.

 Dogo Giɗe dai an ce ya rasu ne a lokacin da yake jinya a Asibitin kwararru Relance da ke garin Sokoto.

Sai dai a wata sanarwa da asibitin ta fitar, ta fito ta bayyana cewa jita-jita da ake ta yaɗawa ba gaskiya ba ne,hasalima Kaf asibitin babu wani majinyaci mai suna Dogo Giɗe, kuma bata bawa mai laifi mafaka.

 “Mun sami labarin cewa an yi ta yada jita-jita a shafukan sada zumunta da sauran kafafe inda ake ta yaɗa cewar riƙaƙen ɗan Ta’adda Dogo Giɗe ya mutu a asibitin mu”.

 “Wannan zance ba gaskiya ba ne,zance ne  maras tushe, asibitin mu bai taɓa jinyar wani mai laifi ba balle kuma ɗan ta’adda.”

“Saboda haka Muna kira ga jama’a da su yi watsi da wannan labarin kuma su daina yaɗa shi saboda karya ne”, Cewar Asibitin.

 Haka kuma Hukumomin asibitin sun nuna yabawan su game da namijin ƙoƙari da jami’an tsaro ke yi na ganin an magance matsalar Ta’addanci da ya addabi yankin,tare da yin kira ga ma’aikatan su da sauran jama’a da su kwantar da hankalin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories